Daga Khalid Yaro da Binta Khalid
Gidan rediyon Premier ya horas da ma’aikatantasa kan rubutu a shafin gidan na Intanet.
An gabatar da horon ne a babban dakin taro na gidan a ranar Laraba, a inda wasu tsaffi da kuma sabbin ma’aikatan gidan suka halarta.
Horon ya kunshi tsarin rubuta rahoto a shafin intanet musamman na gidan.
Malam Yakubu Liman tsohon dan jarida kuma shugaban sashen wasannin kwaikwayo na gidan shi ya jagoranci zaman a ranar, ya kuma gabatar da mukala kan yadda ake rubutun wanda ya banbanta da na radio da Ma’aikatan gidan suka Saba.
Da yadda ake jawo ra’ayin mai karatu, da amfani da hoton da ya dace a labari.
Makasudin horon
“Makasudun wannan horaswa shine gina ku kan tsari ta yadda za ku su gabatar da aikinku na rahotanni cikin takaitacen lokaci, tare da Samun nasara.
“Akwai banbance – banbancen a tsakanin rubun labari na intanet da kuma na watsa wa a radio da talbijin Wanda ya kamata duk dan jarida ya sani don tafiya da zamani.
“Dole ne mai rubutu ya zamanto rubuntunsa ya dace da al’adu da dabi’un jama’ar da yake cikin ta”. Inji shi.
Sannan ya kuma ja hankalin mahalarta horon da su rika yin duba na tsanaki na rubutun nasu kafin su mika ga edita.
A karshe ya ba mahalarta taron shawara da kuma jan hankalinsu wajen yadda za su kula sosai wajen rubutu da kuma wallafa a shafin gidan na Intanet.
Ana sa rai wadanda suka samu horon za su rika aika rahotanninsu shafin intanet na gidan wanda aka sabunta shi, kuma yake karkashin kulawarsa.
Horon na ranar na daga cikin jerin horaswa na kwanaki uku da aka shirya domin inganta aikin sabbin ma’aikatan da kuma wasu tsaffi kan sanin makamar aiki.