Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta nemi a kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi na ba gaira ba dalili a jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a cikinwata sanarwa da kakakinsa Ismaila Uba Misilli, ya fitar a Gombe.
Gwamnan ya bayyana jimaminsa game da wannan mummunan lamarin yana mai bayyana hare-haren a matsayin rashin hankali.
“Irin waɗannan hare-hare na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin Arewa.
“Ana kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka jikkata. In ji shi.
Gwamnan ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Jihar Filato da al’ummarta baki ɗaya.
Sannan ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su ƙara himma wajen kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa an hukunta su.
