Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahotannin cewa tana shirin daukar malamai 3,917
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin ta hannun Daraktan Wayar da Kai na hukumar SUBEB, Balarabe Danlami Jazuli, ta ce labarin ba gaskiya bane.
“Hukumar ba ta taba fitar da wata sanarwa ko umarni na hukuma dangane da daukar malamai ba.
“don haka ina shawartar jama’a su yi watsi da bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta kan wannan batun”, in ji shi.
Jazuli ya kuma bukaci al’umma da su rika tabbatar da sahihancin duk wani Kabari ko sanarwa daga hukumar kafin su yadata.
Labarin da ake yadawa na cewar za a dauki ma’aikatan ne a karkashin shirin “Kano State Government Basic Education Teachers Mapping and Recruitment Plan (2025–2028)”.
