Kungiyoyin dake wakiltar jihar Kano a gasar Premier League ta kasa, Kano Pillars da Barau FC sun gaza samun nasara a wasannin da suka buga a wannan mako.
Barau FC ta yi wasanta a gida Kano ta tashi babu ci da kungiyar Wikki Tourist ta Bauchi.
Ita kuwa Kano Pillars Kashi ta sha da ci 2 ba ko daya a hannun Enyimba International.
Yanzu haka dai Barau FC ce ta biyun karshe a teburin gasar Premier, wato ta 18, yayinda kungiyar Kano Pillars da ta yi rashin nasara ke a karshen tebur, wato mataki na 20.
Masu sharhi kan Wasanni dai na ganin idan kungiyoyin basu yunkura ba, yi za a iya yin abin kunya a wannan shekara, inda duk kungiyoyin ka iya tasowa zuwa gasa mai daraja ta biyu.
