Aminu Abdullahi Ibrahim
Kwamitin sasanta manoma da makiyaya na gwamnatin Kano (L-PRES) karkashin ma’aikatar noma da albarkatun kasa yayi zaman sulhu tsakanin hausawa manoma da Fulani makiyaya dake garin Bagwaro a karamar hukumar Takai.
Zaman sulhun ya biyo bayan rajin jituwa kan zargin cinye burtalai da fulanin yankin suka yiwa manoma.
Yayin zaman sulhun wakilin manoma, Guda Garba, ya zargi fulanin da yinkurin kwace musu gari.
Ya ce fulanin ne ke sako dabbobin su suna cinye musu shuka.
Sai dai a bangaren wakilin Fulani Makiyaya Sabo Ali, ya zargi hausawa manoma da cinye burtalai ta yadda dabbobinsu basa samun gurin kiwo da hanyar wucewa.
Ya bukaci karamar hukuma ta samar da iyaka a burtalai ta yadda zasu rinka kiwo musamman akan manyan duwatsin da dabbobin su ke hawa.
Da take jawabi shugabar kwamitin sasanta rikicin Fulani da makiyayan Zubainatu Abdulrahaman, ta yaba da kokarin shugaban karamar hukumar Takai Muntari Ibrahim Faruruwa, bisa tsarin da ya dauka na kawo karshen rikicin.
Ta ce kwamitin na su zai sake ziyartar garin domin duba cigaban da aka samu sakamakon sulhun da za ayi.
Da yake jawabi shugaban karamar hukumar Takai Muntari Ibrahim Faruruwa, ya ce ya tarar da rikicin tun kafin ya karbi shugabancin karamar hukumar.
Ya ce akwai manyan duwatsu guda biyar da ake fada akansu tsakanin Fulani makiyaya da hausawa manoma kuma tuni karamar hukumar ta dauki hanyar kawo masalaha a lamarin.
Ya ce yaje dakansa har gurin da ake rigima akai kuma yanzu haka ana gab da kawo karshen matsalar.
Muntari Ibrahim Ya bukaci hadin kan Hausawa manoma da Fulani makiyaya don kaucewa shiga duk wani abu da zai janyo tashin hankali.
Daga nan kwamitin na L-Pres ya wuce karamar hukumar Sumaila inda ya ziyarci garin Fajewa tare da duba guraren kiwon dabbobin makiyaya da burtalai da ake zargin manoma sunyi shuka.
Kwamitin na L-Pres karkashin ma’aikatar noma da albarkatun kasa ya sha alwashin cigaba da bibiya tare da sasanta rikicin da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya.
Haka zalika kwamitin ya kunshi jami’an tsaro, wakilan gwamnati, wakilan Fulani, na Fuldan da Miyatti Allah da wakilcin Hausawa manoma da ‘yan jarida.
