
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya soke takardun mallakar filin da ke zama hedikwatar jam’iyyar PDP ta kasa a Abuja.
Wike ya sanar da soke takardun ne a wata wasika mai kwanan wata 13 ga Maris, 2025, wacce ke dauke da taken: “Sanarwar Hakkin Mallaka” mai lamba MISC 81346 dangane da fili mai lamba 243, wanda ke tsakiyar gundumar Abuja.
A cewar ministan, an dauki wannan mataki ne saboda jam’iyyar PDP ta kasa ta gaza biyan kudin hayar fili na tsawon shekaru 20, daga ranar 1 ga Janairu, 2006, zuwa ranar 1 ga Janairu, 2025.
Wike ya bayyana cewa, duk da an sha yin kira ta kafafen yada labarai da jaridu don PDP ta biya duk wani bashin da ake bin ta, jam’iyyar ta kasa biyan hakkokin da ake bukata.
A cikin wasikar da Daraktan Kula da Filaye na FCT, Chijioke Nwankwoeze ya sanyawa hannu, an bayyana cewa:
“An umurce ni da in koma kan haƙƙin mallaka na sama da aka bai wa PEOPLES DEMOCRATIC PARTY (PDP), SAKATAREN KASA, kuma in sanar da ku cewa Ministan Babban Birnin Tarayya na da ikon aiwatar da hurumin da aka ba shi bisa Doka ta 1.8 ta Dokar Filaye ta 19, 2004, ta Tarayyar Najeriya, ta soke haƙƙin mallakar ku, buƙatunku da gata a kan fili mai lamba 243 da ke Central Area, Cadastral Zone A00, Abuja.”
Wannan mataki na nufin PDP za ta rasa mallakar filin, wanda ke zama sakatariyar jam’iyyar a Abuja, sai dai ba a bayyana matakin da jam’iyyar za ta dauka ba dangane da lamarin.