Cikin Kwanaki dari da fara aiki a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC Ltd.), Bashir Bayo Ojulari ya kafa tubalin sabon tsarin gudanarwa na gaskiya, inganci a aiki da kuma samar da sauyi a hada-hadar makamashi.
Tun bayan nadin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi masa a ranar 2 ga Afrilu, 2025, Jagorancin Ojulari ya fara daukar hankalan al’umma, biyo bayan tsare tsaren da ya kawo da za su toshe duk wasu kafofi na rashin gaskiya da sakaci da suka dade suna addabar harkar mai a kasar.
Daya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma a karkashin jagorancinsa shi ne: tabbatar da kammaluwar aikin samar da bututun iskar gas na Ajakuta-Kaduna-Kano ya ketare kogin Neja.
Wannan babban aikin da injiniyoyi ke yi na nuni da jajircewar NNPC wajen fadada hanyoyin samar da iskar gas da bunkasa makamashi mai tsafta a fadin Najeriya.
Kazalika wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ta zarce adadin danyen man da kungiyar kasahe masu arzikin man fetur ta OPEC ta ware mata, inda ake samar da ganga miliyan 1 da dubu 500 da 5 a rana cikin watan Yuni, adadi mafi girma da Najeriya ta samar cikin shekaru biyu da suka wuce.
A cikin gida kuwa, an samu gagarumin ci gaba wajen tabbatar da bututunan man kasar na aiki dari bisa dari a duk lokacin da ake bukatar amfani dasu ba tare da tangarda ba.
Haka zalika, an dawo da fitar da rahotannin hada-hadar kudade da aikace aikacen da kamfanin yake gabatarwa na wata-wata da aka daina tun 2021, tare da biyan kudaden kamfanunuwan da ke da yarjejeniyar hadin gwiwa da NNPCL a kan lokaci.
Ojulari ya bullo da sabon tsari na “A’a Ga Asara” wanda ya hada da rage kashe kudade, dakatar da abubuwa marasa muhimmanci da kuma mai da hankali wajen habaka samun riba.
Daya daga cikin manyan batutuwan da ke kan gaba a wannan yunkuri shi ne duba yadda za a gyara matatun man Najeriya da suka tsufa.
Ojulari ya ce suna duba yiwuwar cefanar da wasunsu ga ‘yan kasuwa.
A bangaren samar da makamashi mai tsafta kuwa, kamfanin ya ba da gudunmawar motocin CNG guda 35 ga shirin shugaban kasa na bunkasa amfani da gas, domin taimakawa wajen samar da sufuri mai sauki da kare muhalli.
Wannan na daga cikin manufofin Ojulari na daidaita ayyukan NNPC da shirin taimakawa daidaita sauyin yanayi a duniya.
Haka kuma, an kara mayar da hankali wajen jin dadin ma’aikata da bunkasa kwarewar aiki.
A yanzu haka kamfanin NNPCL ya tura kudade sama da naira tiriliyan 6.96 zuwa asusun gwamnatin tarayya cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025, yayin da kamfanin ya samu ribar naira biliyan 905 bayan haraji a watan Yuni kadai.
Wannan na nuni da cewa karkashin shugabancin Ojulari, NNPCL na kokarin sake habaka da tsayawa da kafafunsa daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) don kara adadin man da Najeriya ke iya fitarwa da kuma shirin fitar da hannun jarin kamfanin a kasuwa nan da 2028.
Kwanaki 100 na farko na shugabancin Bashir Bayo Ojulari na nuna alamar makoma mai haske ga kamfanin na NNPCL.
