
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ta gudanar da cikakken bincike kan wata mesar da ta kuɓuce daga inda ake kiwonta a gidan tsohon Akanta Janar Ahmed Idris da ke cikin birnin Kano.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a fadarsa yayin da al’ummar unguwar Daneji, karkashin jagorancin mai unguwar Malam Abba Lawan da suka kai masa koke dangane da barazanar tsaron da ke tattare da ajiyar dabbobi masu haɗari a cikin gida a tsakiyar al’umma.
A cewar mai unguwar, tsohon Akanta Janar ya dade yana kiwon namun daji kamar zakuna da kada, da Macizai a gidansa da ke cikin gari tare da yanka musu shanu a fili domin ciyar da su, lamarin da ke haifar da tsoro da damuwa a tsakanin mazauna yankin.
Sarki Sanusi ya bayyana damuwarsa kan wannan al’amari, yana mai jan kunnen Ahmed Idris kan illar kiwon irin wadannan dabbobi masu hadari a cikin gari.
Ya kuma bukace shi da ya gaggauta dauke dabbobin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sarkin ya kuma roki kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, da ya tsaurara bincike kan lamarin, musamman ganin cewa daya daga cikin dabbobin da ake zargin mallakin tsohon Akanta ce ta tsere zuwa cikin gari, lamarin da ka iya janyo mummunan hadari.
A baya-bayan nan dai rahotanni sun bayyana cewa akwai alamun cewa Ahmed Idris na kiwon namun daji ne ba tare da bin ka’idojin kariyar lafiyar jama’a da dokokin kiwon dabba a cikin gari ba.