Gwamnatin tarayya ta gargadi gwamnatocin jihohi da kuma al’umma da su guji kulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga, tana bayyana hakan a matsayin yaudara da ke kawo barazana ga matsalar tsaron kasar nan.
Ministan Tsaro, Janaral Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce gwamnatin tarayya ta dade tana jan hankalin jihohi, ciki har da jihar Katsina, kan hadarin tattaunawa da kungiyoyin dake dauke da makamai.
Ya kuma bukaci al’umma da su daina mu’amala da ’yan bindiga, musamman basu abinci ko wasu kayayyaki, yana mai cewa hakan na taimaka musu ne.
- Gwamnatin Tarayya da ASUU Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniya
- Gwamnan Bauchi Ya Zargi Gwamnatin Tarayya da Amfani da EFCC Wajen Tsangwamar Ƴan Adawa
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Masu Garkuwa da Mutane a Matsayin ’Yan Ta’adda
Janaral Christopher Musa mai ritaya, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta biyan kudin fansa ga wadanda aka sace, yana mai cewa jami’an tsaro na dogaro ne da matakan soja da kuma bayanan sirri wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Ministan tsaron ya kara da cewa, biyan kudin fansa na kara karfafa aikata laifuka, tare da bukatar jama’a su rika kai rahoton sace mutane ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace.
