Wata kungiya da ke ikirarin wakiltar masu amfani da wayar a Najeriya ta yi barazanar maka gwamnatin tarayya a kotu kan kari kudinkiran waya da na data.
Kungiyar ta ce za ta yi hakan ne bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da karin kudin kiran waya da kashi 50 cikin 100 daga watan Fabrairu.
Shugaban kungiyar Adeolu Ogunbanjo ya ce karin kudin ya yi yawa, saboda ‘yan Najeriya na kokawa da tsadar man fetur da kuma farashin kayan masarufi.
“Yayin da na fahimci kalubalen da ake fuskanta a fannin sadarwa, mun amince da ƙarin kuɗin da bai wuce kashi 5% zuwa 10% ba, idan hakan bai wadatar ba, ya kamata kamfanonin sadarwa su nufi kasuwar musayar hannun jari damin tara kuɗaɗe” In ji Ogunbanjo.
“Karin Kashi 50% ya yi yawa, muna cewa ba mu yarda ba, ba abin yarda ba ne, duk abin da ya wuce kashi 10%, za mu kai kara kotu.
Amincewa da karin kudin kiran wayar dai na zuwa ne shekaru 12 bayan da hukumar NCC ta amince da farashin a shekarar 2013. inji rahoton shafin BBC