Daga Hafsat Buhari
Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya umarci tsofaffin shugabannin Jam’iyyar NNPP na ƙananan hukumomin mazaɓarsa da su dawo da motocin da aka ba su tun da sun sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.
Umarnin hakan na kunshe ne cikin wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren ofishin Sanatan, Injiniya Ibrahim Nakwalli Kawaji.
“Motocin da aka raba domin ayyukan jam’iyyar NNPP a kananan hukumomi, dole ne a dawo da su zuwa ofishina”. In ji shi.
Wasiƙar ta kuma ce motocin za su kasance a ofishin Sanatan har sai an warware rikicin cikin gida na jam’iyyar, tare da kira ga shugabannin da su ci gaba da yi wa jam’iyyar hidima da aminci.
Rahotanni sun nuna cewa umarnin ya shafi dukkan shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi da ke Kano ta Tsakiya, ciki har da Dala, Dawakin Kudu, Fagge, Garun Mallam, Gezawa, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Minjibir, Nasarawa, Tarauni, Ungogo da Warawa.
