Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule dake nan Kano ta sanar da cewa ta daina karɓar dalibai a shirin NCE bayan amincewar da hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa NUC da ta baiwa jami’ar izini fara digirin na B. Education.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren harkokin ilmi na jami’ar, Malam Auwalu Mudi Yakasai, ya fitar a madadin magatakardar jami’ar.
Sanarwar ta bayyana cewa an umarci duk masu son shiga jami’ar su nema ta JAMB, sannan su sauya shirin su na yin NCE zuwa digiri, matuƙar sun cika sharuddan shiga jami’ar wanda ya haɗa da samun credits 5 a jarabawar kammala sakandire tare da Ingilishi a matsayin na dole da kuma samun ammaki 150 a jarabawar JAMB.
Wannan matakin na nufin cewa daga yanzu, jami’ar za ta rika karɓar ɗalibai ne kawai zuwa matakin digiri a fannin ilimi.