Kotun Ƙoli ta ƙasar Guinea ta tabbatar da zaɓen shugaban ƙasa, inda jagoran juyin mulkin ƙasar, Mamady Doumbouya, ya lashe zaɓen da tazara mai yawa.
Bayan wannan hukuncin na kotu, tsohon hafsan sojin zai mulki Guinea na tsawon shekara bakwai, ƙasar da ke da arzikin ma’adinai.
Babban zaɓen ƙasar ya gudana ne a ranar 28 ga Disamba, inda Kanal Doumbouya ya samu kashi 86.72 na ƙuri’un da aka kaɗa, duk da cewa wasu jam’iyyun adawa sun ƙi shiga zaɓen.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa wanda ya zo na biyu, Abdoulaye Yero Baldé, ya janye ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Mr Baldé ya zo na biyu da kashi 6.59 na ƙuri’un cikin ‘yan takara takwas da suka yi takara.
