Yayin da ake ci gaba da Shari’ar Rabon gado da waqafi marigayi Sheikh Albaniy Zaria.
Kotun Shari’ar Musulunci ta 1 da ke Tudun Wada, Zariya, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Alkali Jibrin Muhammad Bello, ta kammala gudanar da ziyarar gani da ido (Locus Visit) zuwa wasu kadarori da ake takaddama a kansu dangane da waqafin marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (Rahimahullah).
Shari’ar ta samo asali ne bayan wasu daga cikin iyalan marigayin sun shigar da ƙara a gaban kotun, suna neman a tantance matsayin wasu kadarori da ake ikirarin suna cikin waqafi da kuma gadon da marigayin ya bari.
Masu ƙarar sun kuma nemi kotun ta fayyace matsayin kadarorin da ake takaddama a kansu tare da haƙƙoƙin magada dangane da abin da marigayin ya bari bayan rasuwarsa a shekarar 2014.
A wani mataki na tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin gudanar da ziyarar, kotun ta nemi taimakon jami’an Hukumar Tsaron Farar Hula ta Kasa (NSCDC), waɗanda suka samar da isasshen tsaro a wuraren da aka ziyarta.
Kadarorin da kotun ta ziyarta sun haɗa da gidajen zama, makarantu, filayen ƙasa da sauran kadarori da ke Gaskiya Layout da wasu sassan Zariya da Kaduna, ciki har da Albaniy Science Academy, Saudatu Science Academy, filayen da aka ware domin gina jami’a mai suna Albaniy University of Information and Communication Technology, da kuma filin da aka ware domin gina Albaniy University Teaching Hospital, tare da sauran kadarorin da ake takaddama a kansu.
Ana sa ran kotun za ta karanta rahoton ziyarar gani da ido tare da ci gaba da sauraron shari’ar a zaman da aka sanya ranar 1 ga watan Yuli, 2026.
