Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce kishi da gwagwarmayar dimokuraɗiyya ya mutu a zuƙatan ‘yansiyasar ƙasar nan, kuma a halin yanzu sun kama hanyar hallaka dimokraɗiyya.
Attahirun Bafarawa na wadannan tsokaci ne a lokacin tattauna da manema labarai kan halin da kasar ke ciki.
Ya ce akwai matukar damuwa ganin yadda ake samun mutuwar adawa a fagen siyasar ƙasar nan saboda fifita buƙatun kai.
Sannan ya ce matuƙar aka bar lamura suka cigaba da tafiya a haka, zai iya zama babban nakasu ga makomar al’umma da ma ta ƙasar gaba ɗaya.
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheka da ‘yansiyasar na bangaren hamayya ke yi suna tafiya jam’iyya mai mulki ba don komai suke yi ba na amfanin talaka, face don kansu suke yi, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta mace a kasar a yanzu – babu akida.
Ya bada misalai da galibin ‘yan siyasa da gwamnonin arewa da ya ce duk bukatun kansu suke bai wa muhimmanci, ba wai ciyar da al’umma da raya kasa ba.
