Mai bincike kan zaman lafiya da rikice-rikice, Lekan Olayiwola, ya bayyana cewa kare martabar sarautun gargajiya yana buƙatar tabbatar da adalci da gaskiya idan aka samu zargi kan masu riƙe da sarauta.
A wata maƙala da ya wallafa a TheCable, Olayiwola ya yi tsokaci kan zargin cin zarafin wata baƙuwar yawon buɗe ido da ake yi wa Sarkin Daura, Umar Faruk Umar.
Ya ce bai kamata a ɗauki zargi a matsayin tabbatar da laifi ba, amma kuma bai kamata a bar matsayin sarauta ya zama dalilin hana bincike mai zaman kansa ba.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin bincike tare da sanya takunkumin wucin gadi kan wasu ayyukan Sarkin Daura.
