
Babbar jam’iyyar adawa PDP ta kaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi da kuma kwamitin tsara zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar na shekarar 2027 a yau Alhamis a Abuja.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar rabuwar kawuna tsakanin mambobin kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) kan yunƙurin dawo da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, cikin PDP.
Wasu shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa dawowar Jonathan a yanzu zai iya kawo rikici, yayin da sauya sheƙar Obi zuwa Labour ya rage wa PDP damar samun nasara a zaɓen 2023.
Duk da haka, wasu mambobin NEC sun yi maraba da wannan yunƙuri, suna mai cewa PDP na da isassun jiga-jigai masu ƙwarewa waɗanda za su iya wakiltar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu babu wani tuntuɓa ta hukuma da aka yi wa Jonathan ko Obi kan wannan shirin.