
Uwargidan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Maryam Abacha, ta musanta zarge-zargen da ake yi wa mijinta na wawure dukiyar ƙasa a lokacin da yake mulki.
Matar marigayin ta bayyana hakana ne a wata hira da gidan talabijin na TVC yayin da tsohon shugaban kasar ya cika shekara 27 da rasuwa, a inda ta nanata cewa mijinta bai sace kuɗin Najeriya ba, tana mai cewa da gangan aka sauya manufarsa ta adana dukiyar ƙasar a ƙetare.
Ta ƙalubalanci waɗanda ke zargin mijinta da su gabatar da gamsasshiyar hujja, tare da tambayar ‘yan Najeriya kan yadda suka amince da bayanan da gwamnatocin baya suka faɗa kan karɓo kuɗaɗen da Abacha ya adana a asusun ƙasashen waje.
Gwamnatocin Najeriya daban-daban sun sanar da karɓo makudan kuɗaɗe daga Switzerland, Amurka, da Birtaniya, inda aka yi amfani da su a shirye-shiryen raya al’umma.
Marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranci Najeriya ne ƙarƙashin mulkin soji daga 1993 zuwa 1998.