
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ce, kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka addabi jihar ba baki ba ne, ’yan cikinta ne.
Radda ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
“Akasarin maharan ba baki ba ne, a yankunan danginsu suke, amfani da mutanen yankin na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matasalar tun daga tushe.
“Don haka gwamnatina ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, muka kuma debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe.
“Dalilinmu na kirkirar sabuwar rundunar tsaro ta jiha shi ne mu taimaka wa sauran jami’an tsaro a ayyukansu. Mun dauki mutane daga dukkan yankunan da ke da matsalolin tsaro saboda su suka fi sanin yankunansu da ma mutanen cikinsa fiye da kowa.
“Mazauna wadannan yankunan sun san iyayen ’yan bindigar nan da kakanninsu, saboda ba baki ba ne, wannan ne sirrin samun nasararmu, har muke iya zuwa mu farmake su a har a maboyarsu. Dole sai da dan gari a kan ci gari,” in ji Gwamnan na Katsina.
Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke da makamai kan kai farmaki kan kauyuka su kashe mutanen gari sannan su dauki wasu domin karbar kudin fansa. Sai dai a ’yan kwanakin nan jihar ta dan samu saukin hare-haren.
Daga karshe gwamna ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu sakamakon matakin da gwamnatinsa ta dauka an sami nasarar kama mutane da dama da ke samar wa da ’yan bindigar kayayyaki da kuma bayanan sirri.