Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar afrika CAF, ta sanar da Jerin kasashe 18 da suka samu tikitin buga gasar kwallon kafa ta CHAN ta yan wasan nahiyar afrika.
Gasar CHAN ta yan wasan da suke buga kwallo a cikin gida a nahiyar Afrika, za ta gudana a kasashen Kenya, Tanzania da kuma Uganda daga 1 zuwa 28 ga Fabrairun 2025.
A karshen mako Super Eagle B ta bi sahun kasashen da za su buga gasar ta CHAN bayan do ke Ghana da ci 3-1 a ranar Asabar.
Cikin kasashe 18 da suka samu tikitin buga gasar sun hada da Nigeria, Morocco, Niger, Angola, Madagascar, da masu masaukin baki Kenya, Tanzania da Uganda.
Sauran sune Guinea, Senegal, Mauritania, Burkina Faso, Central African Republic, Congo, DR Congo, Sudan, Rwanda, Zambia.