Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano ta karyata zargin da wasu mazauna unguwar Hotoro Yandodo suka yi na cewa ana shirin sayar da filin maƙabarta da ke yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar, Ambasada Yusuf Imam Ogan Boye ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci filin maƙabartar tare da tawagar Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano.
“Babu wani yunƙurin cefanar da ƙasa, kuma gwamnatin ƙaramar hukumar ba za ta taɓa lamunta irin wannan abu ba”. In ji shi.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano, Comr. Sa’idu Yahaya, ya ce sun ziyarci wurin ne bayan samun ƙorafi daga matasan yankin da ke zargin ana shirin sayar da filin.
Binciken hukumar ya gano cewa babu wani yunƙurin sayar da maƙabartar, yana mai gargadin cewa duk wanda ke da irin wannan niyyar, hukumar ba za ta lamunta da shi ba.
