
Karamar hukumar Nassarawa ta kaddamar da sabon injin zamani na wanke hakori a cibiyar Lafiya a matakin farko dake Gwagwarwa.
Da yake jawabi yayin taron kaddamarwar, Shugaban karamar hukumar Alhaji Yusif Shu’aib Ogan boye ya ce, an samar da na’urar ne domin inganta harkar kiwon lafiya a yankin tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar.
Ogan boye ya kuma yi kira ga ma’aikatan cibiyar lafiyar da su kula da na’urar yadda ya kamata domin amfanin al’ummar karamar hukumar.
A jawabin Shugaban sashen lafiya a matakin farko na karamar hukumar Alhaji Abba Yandi, ya yabawa kokarin shugaban karamar hukumar bisa samar da injin wankin hakorin wanda ya ce zai yi matukar amfani ga al’umma.