Karamar hukumar Nasarawa ta ce babu kamshin gaskiya a zargin da wasu mutane ke yi na zargin mahukuntan yankin da siyar da wani fili da aka ware domin yin makarbta a Hotoron Kudu.
Shugaban Karamar Hukumar Ambasada Yusuf Shu’aibu Imam Ogan Boye ne ya musanta hakan, lokacin da al’ummar hotoron kudu suka kai masa ziyarar gaggawa akan lamarin.
Da yake mika koken nasu, Dagacin yankin, Alhaji Ashiru Abubakar, ya ce sun je ofishin Shugaban karamar hukumar ne domin su bayyana damuwarsu bisa zargin cewa wani mutum yana ikirarin an sayar masa da filin makabartar.
Da yake mayar da martani, Ogan Boye ya ce, babu kamshin gaskiya kan wannan zargin, inda yace gwamnatin Kano mai ci ba ta yarda da sayar da filayen al’umma ba, balle makabarta wadda gida ce ga kowa.
Jami’in yada labaran karamar hukumar ta Nassarawa Sharif Zaharaddin Usman kofar nasarawa ya rawaito cewar, Ogan boye yayi alkawarin gudanar da bincike domin gano gaskiyar
