Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta sanar da dakatar da mai horarwa Usman Abdallah bayan hatsaniya da kuma samun sabani da magoya baya.
A wata sanarwa da sashen yada Labarai na Kungiyar ya fitar a ranar Lahadi, ta bayyana hukuncin dakatarwar da aka yiwa Abdallah zai shafe mako uku sakamakon rashin kokari da kungiyar ba tayi karkashin jagorancinsa.
Pillars karkashin jagorancin shugabanta Aliya Muhd, tace matakin dakatarwar ya zo ne bayan an samu hatsaniya tsakanin Usman Abdallah da kuma magoya bayan kungiyar, jim kadan bayan tashi daga wasan Kano Pillars da Bayelsa United da aka tashi 0-0 a ranar Lahadi.
Kano Pillars wadda ta karbi bakuncin Bayelsa United a wasa mako na 22 a gasar Firimiyar Najeriya ta gaza samun maki uku kan abokiyar karawar ta bayan sun raba maki tsakaninsu.
Kawo yanzu haka Kungiyar ta Kano Pillars ta mika ragamarta zuwa ga Ahmed Garba Yaro-Yaro, kuma zai yi aiki da Abubakar Musa, Gambo Muhammad, Suleiman Shuaibu, da Ayuba Musa da zasu taimaka masa.
A yanzu haka, Kano Pillars za tayi shirin buga wasan mako na 23 a gasar Firimiyar Najeriya da Remo Stars a garin Ikenne, a mako mai zuwa.