Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin jawabinsa a wajen bai wa mata 5,200 jarin dubu Naira 50 wanda ya ke yi a duk wata.
An kuma gudanar da taron ne dakin taro na Coronation Hall a fadar gwamnatin Kano a ranar Talata.
A kuma fadi hakan ne a jawabinsa kuma martani ga kalaman da shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas, kan shirinsu na kwace mulki daga hannun jam’iyyar NNPP a zaben 2027.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa ya fitar yana mai rawaito gwamnan da cewa, aikin hidimta wa Kano ne a gabansa yanzu, ba neman wa’adin mulki na biyu ba.
“Na fi damuwa da sauke nauyin alkawurran da na dauka a wa’adin farko, kuma ina son mutanen Kano su yi min hukunci da ayyukana a karshen mulkina”.
“Masu cewa 2027 zasu kwace mulki daga hannun gwamnatin Kwankwasiyya muna so mu fada musu 2027 ta Allah ce, amma su sani uban kuturu ma yayi kadan ya cutar da Al’ummar Kano”. Inji gwamnan
Tun bayan da jam’iyyar NNPP ta kwace mulkin Kano a zaben 2023, jam’iyyar APC ke shan alwashin dawo da mulkin hannunta a zaben 2027.
A taron bayar da tallafin, gwamnan ya rarraba wa mata tallafin kudi domin dogaro da kansu wanda ya samu halartar dimbin jama’a da kuma manya jami’an gwamnatin da kuma na jam’iyyar NNPP mai mulki.
.