
Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano da Kungiyar masu shirya fina-finai MOPPAN sun cimma matsaya na karin wa’adi kan dakatar da wasu finafinai 22 da hukumar ta yi.
Hakan ya biyo bayan wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar da shugabannin masana’antar Kannywood a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta MOPPAN reshen jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino ya ce daga cikin abubuwan da suka cimma matsaya a tattaunawarsu da hukumar sun hadar da karin wa’adin ci gaba da haska finafinan da kuma sake zama da hukumar don kara samun fahimtar juna.
Kafin cimma wannan matsaya dai, hukumar ta sanar da dakatar da nuna finafinan ne sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar, sannan ta ba masu finafinan mako ɗaya su cika ƙa’idojin hukumar ko kuma gurfanar da su a gaban kuliya.