
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira da a sanya linzami kan amfani da shafukan sada zumunta saboda yadda ake wuce gona da iyaka a amfani da shi.
Sarkin ya yi kiran ne a taron malaman addini da sarakuna da kuma kungoyin addini da aka yi a Kaduna a ranar Alhamis.
“Kowa zai iya wayar gari, ya ɗauki wayarsa ya zagi duk wanda yake so, ko wani da ake girmamawa, ko maƙabcinsa ko ma ɗan’uwa. “Babu dokoki, babu matakin da za a ɗauka kuma babu mai cewa don me, in ji shi.
Sarkin Musulmi wanda Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya wakilta ya kuma bayyana damuwarsa sosai a kan ƙaruwar wuce gona da iri a dandalin a tsakanin malamai,
Sannan ya yi gargadin yadda hakan ke zama babbar barazana ga zaman lafiya da haɗin-kai a kasa.
Taron na kwana daya, ya samu halartar manyan malaman addinin musulunci da sarakuna da kuma kungiyoyi daban-daban.