
Mai unguwar Shagari Quarters a nan Kano Alh. Zubairu Muhammad ya ce, yan majalisu na da rawar da za su taka wajen samar da dokar da za ta hana cin zarafin ‘ya’ya mata a kasar nan.
Alh. Zubairu ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki da cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma CITAD ta shirya don tattauna hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen cin zarafin mata, domin ba su damarmakin da za su gudanar da rayuwarsu cikin farin ciki da walwala.
Mai unguwar Shagari Quarters ya ce, matuƙar yan majalisu suka samar da dokar hana cin zarafin al’umma babu shakka za’a samu raguwar masu aikata laifuka nau’i daban daban.
A nasa bangaren limamin masallacin juma’a na rundunar ‘yan sanda shiyya ta daya, a nan Kano Muhammad Kabir Abubakar ya yi jan hankali ga ma’aurata a musulunci da su himmatu wajen sauke nauyin “ya”yansu da Allah ya ɗora masu don samun al’umma ta gari.
Primier Radio ya rawaito cewa manufar taron shi ne kokarin kawo karshen cin zarafin jinsi bisa la’akari da gatan da Addini, Al’ada da Shari’a suka yiwa yaya mata.
Taron ya samu halartar shugabannin Addinin Islama, Kirista, Malaman Makaranta, masu rajin kare hakkin ɗan Adam, ƙungiyoyin direbobi, masu Unguwanni da ‘yan jaridu.