Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa (NHIS) Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana saboda sukar manufofinta.
Farfesan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a gidan gyaran hali na Kuje inda yake tsare
Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa, amma ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa tuggu ne na siyasa.
Yusuf, wanda ke tsare a Kuje, ya ce tuhumar babu tushen shari’a, kuma an shirya masa ne don rufe masa baki.
Kama Farfesan ya jawo suka daga ’yan adawa da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, inda suka yi zargin cewa ana murƙushe ’yancin faɗar albarkacin baki.
