
Majalisar Dokokin jihar kano ta ce, kama masu karya dokokin hanya ba aikin hukumar KAROTA bane, aikin ta shine kula da tabbatar da masu ababan hawa suna bin titi ba tare da an samu cunkoso ba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na majalisar a ranar Talata.
“Da yawa daga cikin ayyukan da hukumar KAROTA ke gudanarwa a yanzu ya saɓa da tanadin dokar da ta samar da ita musamman kama mutanen da suka aikata laifuka akan titi”. In ji shi.
Majalisar ta tabbatar da cewa za ta sanya idanu wajen ganin hukumar KAROTA ta tsaya kan hurumin dokar da ta samar da ita tun a farko.