Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0
Ta yi hakan ne a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano.
Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya ƙara ta biyu a minti na 72 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Wannan nasarar ce ta uku da Barau FC ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana.
Ta kuma yi kunnen doki a wasanni huɗu, aka kuma doke ta a biyar.
Yanzu haka Barau FC ta hau mataki na 16 a teburin gasar da maki 13, yayin da Enugu Rangers kuwa ta koma mataki na 14.
Aminiya ta rawito cewa, ranar Laraba, Barau FC za ta kece raini da Rivers United a kwantan wasan mako na biyar da za a buga a filin wasa na Sani Abacha.
A wani kwantan wasan mako na biyar, Kano Pillars za ta yi tattaki zuwa filin wasa na Remo Stars domin ɓarje gumi.
