Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam’iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027,
inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam’iyyar ya tsaya takara.
Sule Lamido ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da gidan talabijin na Channels
Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu’amalanci mulkin ƙasar.
Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana batun wanda za su tsayar a zaɓen wanda ke tafe.
Wannan jawabin na Lamido na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da yaɗa raɗe-raɗin cewa Jonathan zi tsaya takara a zaɓen mai zuwa domin fafatawa da Bola Tinubu.
