Daga Safina Abdullahi Hassan
A wani rahoton Asusun Yara Na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), mata da dama a ƙasashen Afirka ta Kudu da kuma yankin Sahara ba sa zuwa makaranta duk lokacin da suke jinin al’ada saboda rashin samun auduga mai tsafta.
Rahoton ya kuma nuna cewa wannan matsala tana kawo cikas ga ci gaban ilimi da kuma damar shiga cikin al’umma ga ‘yan mata, abin da ke iya rage damar su ta samun cigaba a rayuwa.
Masana harkar lafiya sun bayyana damuwa kan yadda mata da yawa ke ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon amfani da kayan da ba su dace ba a lokacin al’adarsu.
Sun ce wannan hali kan jawo kamuwa da cututtuka a matuncinsu da kumburin gabobi da ciwon mara da ciwon kai, har ma da matsalolin haihuwa.
Dakta Aisha Umar, wata likita a jihar Kano, ta yi karin haske kan lamarin.
“Mata da yawa na amfani da tsumma ko takarda ko kayan da ba su da tsafta saboda rashin auduga mai kyau. Wannan na iya haifar da cututtuka masu tsanani da ke shafar lafiyar mace gaba ɗaya.
“Akwai bukatar gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula su ƙara ƙoƙari wajen ilmantar da jama’a da kuma samar da kayan tsafta ga ƴan mata a makarantu da al’umma.” In ji Likitar.
Kan haka, kungiyar Population Services International (PSI) ta ƙaddamar shiri na musamman na wayar da kan jama’a musamman ‘yan mata kan illolin rashin amfani da auduga mai tsafta a lokacin al’ada.
Shirin na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na taimaka wa mata da ƴan mata su kare kansu daga cututtuka da ke biyo bayan rashin tsaftar jiki yayin jinin al’ada, musamman a yankunan da ake fama da ƙarancin kayan tsafta.
Da kuma ƙarfafa fahimtar cewa jinin al’ada ba abin kunya ba ne, illa ma wani ɓangare ne na lafiyar su.
Kasancewar jinin al’ada wani muhimmin al’amari ne a bisa yanyin halitta, da ke nuna lafiyar jiki da tsarin haihuwa na mace.
PSI ta bukaci gwamnati ta samar da kayayyakin tsafta a makarantu da asibitoci, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen kan tallafawa mata a lokutan al’ada.
Kungiyar ta kuma yi kira ga iyaye da mazaje da su daina kallon jinin al’ada a matsayin abin kunya, domin jinin al’ada wani ɓangare ne na rayuwar mace.
Don haka, ana bukatar kulawa, fahimta, da tallafi daga al’umma domin tabbatar da cewa babu mace ko yarinya da za ta rasa damar zuwa makaranta ko aiki saboda al’ada.
