Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta kama mutune 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban-daban a sassa na jihar.
Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar daga Dutse, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar, an kama waɗanda ake zargin ne a wurare da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da Yankwashi.
Rundunar ta kuma ƙwato miyagun ƙwayoyi iri daban-daban da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam, Sholisho, Sukudayin, tabar wiwi, da kuɗi har Naira 235,225.
SP Shiisu ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike tare da kama duk wanda ke da hannu a irin wannan harkar.
Ya ƙara da cewa, da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa laifukansu.
