Ta kuma zarge shi da amfani da makamai masu guba a fadan a yakin da suke yi da RSF
Amurka ta sanya wa Shugaban Sojin Sudan, Adel Fattah al Burhan, takunkumi saboda rawar da yake takawa a yakin basasar da ke faruwa a kasar.
Wannan mataki ya biyo bayan takunkumin da aka sanya kan kwamandan dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, a makon da ya gabata.
Amurka ta zargi dakarun Sudan da ci gaba da amfani da makamai masu guba a yakin basasar da ke gudana, wanda ya jefa kusancin rabin al’ummar Sudan cikin yunwa tun daga shekarar 2023.