
Jam’iyyun adawa na ƙasar nan PDP, NNPP da ADC sun yi watsi da shirin Hukumar Rabon Kuɗaɗen Ƙasa (RMAFC) na ƙara albashi ga shugaban ƙasa, mataimakinsa, ministoci, gwamnoni da sauran manyan jami’an gwamnati.
An bayyana wannan shiri a ranar Talata, inda hukumar ta ce tana shirin sake nazarin tsarin albashin shugabanni domin daidaita shi da yanayin yau.
Sai dai jam’iyyun adawa sun yi kaca-kaca da wannan mataki, suna mai cewa ya nuna rashin tausayi da kuma rashin dacewa a wannan lokaci da tattalin arzikin ƙasa ke ƙara tabarbarewa.
Sun ce mafi yawan ‘yan ƙasa na fama da yunwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙarancin kuɗin albashi.
Sakataren yaɗa labarai na ADC a matakin ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana lamarin a matsayin shaida ta yadda shugabanni ke rayuwa cikin walwala ba tare da la’akari da irin matsalolin da jama’a ke fuskanta ba.
A nasa ɓangaren, shugaban NNPP na Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya ce shirin na nuni da yadda gwamnati ke wulakanta damuwar talakawa.
Haka kuma, mataimakin shugaban matasa na PDP a ƙasa, Timothy Osadolor, ya yi zazzafar suka, inda ya ce matakin na nuna rashin tausayi da shugabannin ƙasa ke yi.