
Jam’iyyar NNPP reshen karamar hukumar Tudun Wada ta zargi jami’iyyar adawa ta APC da kokarin tayar da rikici a yankin.
A labaran mu na baya dai mun kawo muku korafin wasu mutanan yankin wadanda suka zargi shugabar karamar hukumar ta Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Salisu Soja ta yi amfani da yan daba wajen tashin su daga wuraren da suke yin sanao’insu.
Sai dai shugaban jami’iyyar NNPP na karamar hukumar Tudun Wada, Dalha Idris Sumana, ya ce zargin da mutanen suka yi ba gaskiya ba ne.
Wannan danbarwa ta sa Rundunar Yan sandan Kano gayyatar shugabar karamar hukumar a ranar Talatar da ta gabata domin fadada bincike.
Sai dai kawo yanzu rundunar yansandan bata fitar da wani Karin bayani ba.