Jam’iyyar adawa ta ADC ta zargi hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da yunƙurin dakatar da ita daga gudanar da tarukanta domin zaɓen shugabanninta.
ADC tsagin David Mark ta yi watsi da gargaɗiin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi, tare da jaddada aniyar ci gaba da tsare-tsarenta na gudanar da zaɓukan shugabanninta na jihohi da babban taron jam’iyyar na ƙasa.
A baya-bayan nan ne dai INEC ta gargaɗi jam’iyyar da kada ta gudanar da tarukan jam’iyyar da za su zaɓi shugabanninta don gudan Matsala har sa an warware rikicin shugabancin daya kunno kai a jamiyyar.
Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise a ranar Juma’a shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ya ce kotu ta riga ta dakatar da jam’iyyar daga gudanar da komai har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar.
Sai dai Kakakin jam’iyyar, Faisal Kabir ya shaida wa kafar BBC cewa, matakin wata ƙullalliya ce domin dana wa jam’iyyar tarko a hana ta yin tarukan ta yadda daga baya za a ce ba ta da shugabanci, don haka ba za ta shiga zaɓen 2027 ba.
Ya ƙara da cewa abin da dokokin Najeriya suka ce shi ne ka sanar da INEC taron jam’iyyarka kwana 21 kafin ranar taron, mu kuma mun riga mun sanar da ita.
