
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta amince da buɗe sabbin shirye-shiryen digiri guda 28 ga Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule da ke Kano, lamarin da ke nuna ci gaba mai ma’ana tun bayan sauyinta daga Kwalejin Ilimi zuwa cikakkiyar jami’a.
A cewar wata sanarwa da magatakardar jami’ar kuma sakataren harkokin ilimi, Dr. Mudi Yakasai, ya fitar, an samu amincewar ne bayan tantance cikakken tsarin karatu, ƙarfin ma’aikata da kuma ingancin kayan aikin da jami’ar ke da su.
Ya bayyana cewa za a fara gudanar da sabbin shirye-shiryen ne daga zangon karatu na 2025/2026.
Daga cikin darussan da aka amince da su akwai; Ilimin manya, Ilimin yara da na firamare, Ilimin zamantakewa da tarbiyya, Ilimin kasuwanci, Ilimin harsuna da al’adu, Addinin Musulunci da Kiristanci, Tarihi, Ilimin fasaha da kirkire-kirkire, Ilimin kiwon lafiya, Noma, Tattalin arziki, Siyasa, da Ilimin taswirar ƙasa.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sauya matsayin makarantar daga tsohuwar Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Kano (Federal College of Education, Kano) zuwa Jami’ar Ilimi, mai taken sunan sanannen ɗan siyasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Yusuf Maitama Sule.