Ahmad Hamisu Gwale
Jami’ar Bayero dake nan Kano, ta daga likkafar Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo zuwa Farfesa a fannin Hadith.
Rahotanni sun bayyana jami’ar ta Bayero ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Juma’ar data gaba.
Shafin Facebook na Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ne ya wallafa hakan, a ranar Juma’a da ke tabbatar da daga likkafar Malamin zuwa Farfesan Hadith.
Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo, na daya daga cikin manyan Malaman addinin Musulunci a Najeriya da suka shahara kuma suke koyar da al’umma addinin Musulunci.
Sheikh Sani Rijiyar Lemo, wanda ke koyarwa a jami’ar Bayero sashin addinin Musulunci, haka zalika ya shahara wajen koyar da al’umma tafsirin karatun Al-Qurani mai girma a ciki da wajen kasar nan.