Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna.
Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna.
A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u
A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci.
A wata sanarwa da kakaki rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabi’u Muhammad, ya yaba wa haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda ya bayyana kama mutumin a matsayin wani muhimmin mataki na kare martabar zabe.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin kawo cikas ga zaben, zai fuskanci hukunci ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
