Sabon Ministan Tsaro Janar Christopher Musa Mai ritaya, ya ce zai yi duk abin da ya kamata a yaki da ta’addacin da ya addabi kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai jim kadan bayan da majalisar dattawan kasar nan ta kammala tantance shi.
“Zan yi amfani da kwarewar da nake da ita tare da yin aiki da hukumomin tsaro domin dakile dukkanin wata barazanar tsaro a kasarnan.
“Akwai bukatar kowa da kowa ya sa hannu wajan tallafa wa yunkurin gwamnati da kuma hukumomin tsaro domin dakile hare-haran yan bingidar.
Ministan ya sake jadadda kiran sa ga al’ummar kasar nan da su ci gaba da bawa jami’an tsaro hadin kan da suka da bukata musamman wajan basu rahotannin sirri da zarar sun ga wata bakuwar fuska da basu amince da ita ba.
