Tsohon ma’aikacin gwamnati jihar Kano, Alhaji Bello Abdullahi, Sarkin Shangu Murabus, ya sadaukar da kudin fanshonsa domin tallafawa gina masallacin Juma’a a unguwarsu ta Shangu, karamar hukumar Rano.
Alhaji Abdullahi Bello, wanda shi ne Hakimin Shangu, ya sanar da wannan gudunmawa, yana mai cewa masallacin zai zama cibiyar koyar da ilimin addinin Musulunci da kyawawan dabi’u ga matasa.
Ya bayyana wa Sarkin Rano, Mai Martaba Ambasada Muhammad Isa Umaru, cewa kudin fanshon mahaifinsa ya kai kimanin Naira miliyan biyar.
Sarkin Rano ya bayar da izinin fara aikin ginin, yana mai yaba wa Alhaji Bello Abdullahi bisa wannan karamci da kishin al’umma, tare da jaddada muhimmancin hada kai wajen gudanar da aikin.