Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana matukar damuwarta da matakan da gwamnatin Jihar Lagos ta ɗauka na rusa ɗaruruwan shaguna a babbar kasuwar Alaba Rago dake ƙaramar hukumar Ojo.
Amnesty ta ce hukumomin Lagos ba su bi ka’ida ba wajen tatatunawa da waɗanda abin ya shafa da kuma samar musu mafita kafin wajen rusa shagunan.
Ƙungiyar ta ce gwamnati ta bai wa mazauna shagunan wa’adin wata guda ne kacal, maimakon watanni shida da doka ta tanada, kafin rusa musu shagunan, abinda ke nuna karya doka da kuma take hakkin Bil Adama.
Amnesty ta ce matakin na gwamnatin Lagos ya jefa daruruwan iyalan masu shaguna cikin ƙunci saboda rasa muhallin su, da kuma hanyar su ta samun abinda za su ci, bayan sun kwashe dogon lokaci suna gudanar da sana’o’in su a wurin.
Ƙungiyar ta ce irin yadda aka yi amfani da ƙarfi wajen rusa shagunan, ya taimaka wajen jikkata wasu masu shagunan a wurin, baya ga rasa shaguna da kuma hajjojin da suka mallaka.
Amnesty ta yi zargin cewar, yunkurin wasu masu shagunan na ceto kayan da suka mallaka ya gamu da fushin jami’an tsaro, waɗanda suka harba musu hayaƙi mai sa hawaye.
Ta ƙara da cewar, daruruwan masu shaguna suna kallo ana lalata musu dukiya, ba tare da ɗaukar matakin ceto su ba, a kasuwar da ake da tarin marasa ƙarfi waɗanda ke gudanar da harkokin kasuwancin su, domin samun abinda za su dogara da shi.
Amnesty ta tuna wa gwamnatin jihar Lagos cewar, dokokin duniya sun haramta amfani da ƙarfi wajen lalatawa jama’a dukiyoyin su, saboda haka ta bayyana irin halin da waɗannan ƴan kasuwar Alaba Rago suka shiga a matsayin na tada hankali tare da cin zarafi.
Sanarwar ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar Lagos da ta gaggauta kafa kwamitin bincike domin gano irin aika aikan da aka yi a kasuwar Alaba Rago da zummar biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa wajen rasa shaguna da gidaje da kuma dukiyoyin su.
