
Daya daga cikin maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Filato ta tsinci Dala 5,000 ta kuma mayar wa da mai shi.
Matar mai suna mai suna Hajiya Zainab Idris daga jihar Plato ta tsinci kudin ne a birnin Makka.
Rahotanni sun nuna matar ta tsinci kudin ne wanda aka gano cewa guzirin maniyyacin ne a dan kasar Tajikistan a cikin Masallacin Harami a ranar Talata.
Jimlar kudin Dala dubu biyar, kimanin Miliyan Takwas da Dubu Dari Biyu, idan aka canza zuwa Naira a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban Hukumar ta Jihar Filato, Honorabul Dayyabu Dauda duk sun tabbatar da faruwar lamarin.
“Ta nuna halin dattaku, gaskiya da rikon amana ta hanyar mayar da Dala dubu biyar din da ta tsinta a masallacin harami ga mai su. Hakika ta nuna halin nagarta da tausayi,” in ji Honorabul Dayyabu.
Takuici
Rahotanni sun ce sakamakon halin gaskiya da wannan mata ta nuna mutanen kasar sun yi alkawarin gina masallaci da makaranta a jihar Plato.