Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da samar da wadataccen ruwan sha a birnin jihar, tare da ci gaba da aiwatar da ayyukan more rayuwar da za su amfanar da al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci Mauludin da Madrasatul Dr Adam Kamaluddeen Adam Nama’aji ta shirya.
Gwamna Abba ya ce tuni an baiwa wani kwararren kamfani kwangilar farfado da manyan tashoshin samar da ruwa na Tamburawa da Challawa, inda ake gudanar da aikin dare da rana domin dawo da tabbataccen ruwan famfo a birnin Kano.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da gyaran tashoshin ruwa a yankunan karkara, inda wasu ayyukan tuni aka kammala kuma suke samar da ruwa, yayin da ake kan kammala wasu, inda daga cikin waɗanda suke aikin samar da ruwan akwai tashar Guzugu da ke Kabo, Joɗa da ke Gabasawa, da kuma tashar Wudil.
Da yake jawabi a wajen taron, Khalifa Dr Adam Kamaluddeen Adam jinjinawa gwamnatin Gwamna Yusuf kan ayyukan raya ababen more rayuwa, musamman gina hanyoyi a sassa daban-daban na Kano, musamman ƙoƙarin da gwamnati ke yi na farfado da tashoshin ruwan Tamburawa da Challawa.
