Iran ta soke zaman tattaunawa da ya kamata ta yi da Amurka kan batun nukiliyarta a Oman gobe lahadi sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai mata a jiya juma’a, kamar yadda kakin ministan harakokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana cikin wata sanarwa.
Ministan harakokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce babu bukatar ci gaba da tattaunawa da aka faro tsakiyar watan Afirilun wanan shekara lura da harin dabbanci da Isra’ila ta kai mata.
Kafofin yada labarai da dama a Iran sun shaida cewa guda daga cikin masu baiwa jagoran addinin musluncin Iran Ayatollah Ali Khamenei shawara, kuma mai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar, Ali Shamkhani, na daga cikin wadanda su ka ji rauni a hare-haren na Isra’ila.
Masana siyasar duniya na kallon harin da Isra’ila ta kai kan Iran a matsayin tsararren abu domin kawo cikas ga shirin tattaunawar da aka shirya gudanarwa a gobe lahadi.
ƙasashen duniya dai sun yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa, inda kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi zaman gaggawa kan lamarin Jiya Jumma’a.
