
Iran ta sanar da janyewarta daga yarjejeniyar da ta kafa Hukumar Kula Da Yaduwar Makamin Nukiliya ta Duniya (IAEA) a bisa zargin shugaban hukumar Rafael Grossi da nuna son kai da rashin adalci ga ƙasar.
Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ne ya bayyana cewa matakin majalisar dokokin ƙasar na ƙaɗa ƙuri’ar janyewa daga yarjejeniyar ya samo asali ne daga yadda Grossi ke tafiyar da al’amuran hukumar cikin rashin daidaito da tsangwama.
A cewar Pezeshkian, Iran ba za ta ci gaba da hulɗa da IAEA ba, musamman a bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan tashoshin nukiliyar ƙasar a ranar 13 ga Yuni, wanda ya haddasa asarar rayuka da lalacewar muhimman cibiyoyi.
Iran ta ce Grossi ya gaza yin tir da hare-haren, lamarin da ya kara dagula dangantaka tsakanin Tehran da hukumar.
A yayin da Grossi ke bayyana cewa Iran na da duk ƙwarewar da ake buƙata domin dawo da aikin tace sinadarin Uranium nan da watanni masu zuwa, Iran ta ce hakan ba zai yiwu ba sai an tabbatar da tsaron cibiyoyin nukiliyar ta.
Majalisar dokokin Iran ta amince da dokar dakatar da hulɗa da IAEA, kuma majalisar kula da doka ta ƙasar ta tabbatar da sahihancin dokar, wanda ke nufin cewa Iran ta dakatar da duk wata hulɗa da hukumar a hukumance.
A gefe guda, ana ci gaba da nuna shakku kan ikirarin gwamnatin Amurka da Pentagon cewa sun lalata dukkan cibiyoyin nukiliyar Iran, musamman bayan rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin cibiyoyin da ke karkashin ƙasa ba su samu rauni ba.
Wannan rikici na kara jefa shirin hana yaduwar makaman nukiliya cikin ƙalubale, tare da barazana ga zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.