
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da jawabinsa ga al’ummar kasa a ranar tunawa da ‘yancin kai na Nijeriya karo na 65.
A cikin jawabinsa, ya bayyana ci gaba a fannin tattalin arziki, tsaro, da kuma yaba wa sojoji saboda “nasarar yakar ta’addanci da ‘yan bindiga, da sauran laifuka,” inda ya ambaci nasara a kan “Boko Haram a Arewa-Maso-Gabas, IPOB/ESN a Kudu-Maso-Gabas, da ‘yan bindiga da sace-sace.”
Bayanin sanya IPOB da Eastern Security Network (ESN) a matsayin kungiyoyin ta’adda ya jawo cece-kuce daga IPOB.
Kungiyar ta fitar da sanarwa kin amincewa da jawabin, tana mai cewa yana cike da “kyi” da “raba kan jama’a.”
Kungiyar, karkashin jagorancin Mazi Nnamdi Kanu da ake tsare, ta zargi Tinubu da Karyar cewa IPOB kungiyar ta’adda ce, IPOB ta jaddada cewa ita “kungiya ce ta zaman lafiya, wadda duniya ta amince da ita, tana neman ‘yancin kai ta hanyar da ba ta da tashin hankali,” ba kamar kungiyoyin ISWAP ko Al-Qaeda ba, wadanda Tinubu bai ambata ba.
Sanarwar ta nuna rashin amincewa da Tinubu saboda rashin magana a kan tashin hankalin Fulani a jihohi kamar Kwara, Plateau, Benue, da Enugu, yayin da ya ke mayar da hankali kan IPOB kadai.
IPOB ta kwatanta jawabin a matsayin yunƙurin “taimakawa al’ummar Igbo ta hanyar farfagandar gwamnati,” wanda ya samo asali daga sha’awar Birtaniya da “yan Igbo masu goyon bayan siyasa.”
Sun Kuma yi gargadin cewa irin wannan magana ta sabawa kundin tsarin mulkin kasa da ke kare ‘yancin kai kuma na iya haifar da tashin hankali.
Sanarwar IPOB mai taken “Mun Ki amincewa da Jawabin Tinubu Mai Cike da Kyi na Ranar ‘Yancin Kai,” wanda aka saki a ranar 1 ga Oktoba, 2025, ya kira ga al’ummar duniya da su lura, kuma ya sake jaddada gwagwarmayar Biafra a matsayin “mai tushe a gaskiya, adalci, da ‘yancin kai.”