Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da dage aikin sabunta bayanan masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasa har sai bayan zaɓen gama gari na shekarar 2027.
Sanarwar ta fito ne bayan wani taro da Hukumar ta gudanar da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohin kasar nan a Juma’ar nan, 10 ga Afrilu, 2026, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin zaɓe.
Hukumar INEC ta bayyana cewa, aikin sabunta bayanan na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihanci da ingancin rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta ƙasa.
Aikin zai haɗa da tantance bayanan masu rijista, cire maimaitattun sunaye da waɗanda ba su cancanta ba, tare da bai wa masu zaɓe damar duba bayanansu da yin gyara idan akwai kuskure.
Hukumar ta kuma jaddada ƙudirin ta na ci gaba da gudanar da zaɓe cikin ‘yanci, gaskiya da sahihanci tare da tabbatar da haɗa kowa da kowa a harkar zaɓe.
